18 Yuli 2020 - 11:38
WHO Ta Bukaci A Kara Azama A Yaki Da COVID-19

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci a kara azama game da daukar matakan rage tasirin annobar COVID-19 a yankunan da suka fi tsananin bukatar tallafin jin kan bil adama a dukkan yankunan kudu da hamadar Sahara dake Afrika domin rage munanan illolin da matsalar ka iya haifarwa.

ABNA24: Da take sanar da hakan, daraktar hukumar WHO ta shiyyar Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce al'ummomin dake fama da matsalolin tashe tashen hankula da bala'u daga indallahi a nahiyar suna bukatar kulawa ta musamman wanda ya dace a baiwa mutane marasa galihu a yayin da ake yaki da annobar COVID-19.

Yankin kudu da hamadar Sahara dake Afrika yana da sama da kashi 26 bisa 100 na yawan 'yan gudun hijira na duniya baki daya, kuma akwai kimanin mutane miliyan 19 wadanda rikice rikice ya tilastawa ficewa daga matsugunansu.

Ta bukaci a kara zuba kudade masu yawa a fannin gwaje gwajen cutar COVID-19, da warware matsalolin mutanen da tashe tashen hankula ya shafa a Afrika.

A halin da ake ciki dai MDD, ta sake neman tallafin Dala Biliyan 3.6 domin tunkarar shirinta na jin kai a duniya a daidai wannan lokaci da ake fama da annobar korona.

342/